Isa ga babban shafi
Najeriya

Fiye da mutane 16 suka mutu a gumurzun neman aikin yi a Najeriya

Rahotanni daga tarayyar Najeriya na nuna cewar akalla mutane 16 ne suka mutu a wani gumurzun neman ayyukan yi na Gwamnatin tarayyar Najeriya

Gumurzun neman aiki a Najeriya
Gumurzun neman aiki a Najeriya facebook
Talla

Daruruwan mutane ne aka raunata a wannan Gumurzu da aka yi a ranar Assabar, inda wasu da suka tsallaka Rijiya da baya suka shaidawa Kamfanin Dillancin labarai na AFP cewar Dubban mutane ne suka gabatar da bukatar neman ayyukan yi da hukumar kula da shige da ficen Baki ta kasar a Dandalin taro na babban birnin tarayyar Najeriya da ke Abuja.

Shaidun gani da Ido sun bayyana cewar matsalar ta faru ne sakamakon tarmutsitsin da ya faru tsakanin Dubban manema ayyukan yi, a yayin da aka buda kofa Daya kacal a Dandalin da masu neman aikin yi Dubu 60 suka halarta.

Assibitocin Gwamnati ma a babban birnin tarayyar sun kama ture wadanda suka ji rauni dole saboda rashin wurin ajiye su, sakamakon yanda kusan daukacin Assibitocin suka cika da masu rauni daga Dandalin neman ayyukan yin.

Wata matashiya data farfado a Gadon Assibiti ta koma kukan yanda ta rasa Takardun kammala karatunta na ainihi da ta zo da su a wurin neman aikin.

Yanzu haka dai Ministan harkokin cikin gida kan mutuwar matasan masu neman aikin da aka samu a karshen mako, sai dai ministan cikin gidan Abba Moru ya zargi matasan ne da kin bin ka’ida, abinda ya haifar da tirmitsitsin da ya kaiga rasa rayukan.

Minsitan yace matasa 520,000 suka shiga neman guraban aikin 4,556, amma kuma suka ki bin ka’idar da aka shata musu.

Musa Yashi Babawo na daya daga cikin matasan da suka tsallake rijiya da baya a garin Bauchi, ya kuma ce a gaskiya Ministan bai yiwa Matasan Najeriya adalci ba, ganin yanda ba’a ingantaccen tsari na ajiye masu bukatar ayyukan yin ba, abinda ya haifar da wannan matsalar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.