Isa ga babban shafi
Najeriya

Kusan mutane 50 suka mutu a rikicin jihar Pilato ta Nijeriya

Harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a karamar hukumar Langtang ta jihar Pilato a taraiyyar Nigeria, da kuma bata kashi tsakanin sojoji da maharan, ya yi sanadiyyar mutuwar kusan mutane 50 yayin da aka kone gidaje da dama. Rahotanni na cewa da alama harin na jiya Alhamis, na da alaka da ramuwar gayya, sakamakon satar shanu, lamarin da ke yawan kawo tashe tashen hankula a yankin tsakiyar Nigeria.Mai magana da yawun rundunar Sojan da ke aikin wanzar da zaman lafiya a yankin, Captain Salisu Mustapha ya ce ‘yan bindigar sun far wa kauyuka 3, a karamar hukumar ta Langtang.Captain Mustapha ya ce maharan sun hallaka kauyawan 28, yayin da 20 daga cikin maharan suka mutu, sakamakon fito na fito da soja, da suka kai dauki cikin gaggawa.Ya ce an kama 2 daga cikin maharan, da suka far wa kauyukan Karkashi, Bolgang da Magama.Dubban mutane ne suka mutu a ‘yan shekarun nan a jihar ta Pilato, sakamakon fadace fadacen da ke da alaka da kabilanci da addini.Ana ci gaba da samun yaduwar makamai a taraiyyar Nigeria a baya bayan nan, lamarin da ke jawo tashe tashen hankulan da hukumomi suka gagara kawo karshen su. 

IRIN
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.