Isa ga babban shafi
Najeriya

Harin roka ya kashe dan shekaru 10 a Jihar Pilato

Wani harin roka da aka yi niyyar ya samu wata makarantar Islamiyya a garin Bukuru da ke Jos ta Kudu a Jihar Pilato ya yi sanadiyar mutuwar wani yaro dan shekaru 10.Wadanda da aka yi abin a kan idonsu sun ce wani mutum sanye da jar riga ya harba roka wacce ta kauce ta fada a wani gida da ya sami yaron akai wanda hakan ya yi sandiyar mutuwarsa. 

Gwamnar Jihar Pilato, Jonah David Jang
Gwamnar Jihar Pilato, Jonah David Jang
Talla

Mai Magana da yawun gwamnatin Jihar Pilato, Pam Ayuba, ya tabbabatarwa Kamfanin Dillancin labaran Faransa cewa harin an yi niyyar ya samu makarantar Nurul Islam a yayin da dalibai ke shirin jarabawa.

A cewar mai Magana da yawun ‘Yan sandan Jihar, Eammanuel Abuh, wanda ya kai harin daga tsallaken titin da ya raba yankin Musulmi da Kiristoci ya tsaya ya kuma harbo rokar.
A ‘yan kwanakin nan kuma an kwance wani bam a yankin kamin ya tashi.

Wani mazaunin angwur da abin ya faru, Murtala Abdullahi ya ce, wanda ya harba rokar ya ruga da gudu ya shiga anguwar Kiristoci, wanda hakan hukumomi ba su tabbatar ba.

Mai Magana da yawun bakin rudunar sojoji da aka girke a garin Jos domin wamzar da zaman lafiya, SalihuMustapha ya nuna damuwar sa kwarai ganin cewa yanzu fararen hula na iya samun manyan makamai irinsu RPG wacce it ce aka harba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.