Shirin Duniyar wasanni ya leka ne gasar kwallon Dawaki ta Polo da aka kammala a birnin Lagos shiyar kudu maso yammacin Najeriya. A ranar 27 ga watan Fabrairu ne aka bude gasar a birnin Lagos wanda kuma aka kammala kuma a ranar Lahadi 10 ga watan Maris.
Talla
Jerin Gasa kusan guda shida ne aka gudanar wadanda suka kunshi gasar lashe kofin Dansa da gasar sarkin Lagos wato Oba Cup, akwai Italian ambassadors Cup da independent cup da kuma gasar lashe babban kofi na Majekudomi. A cikin Shirin za ku ji Jihar Kano ta lashe kofuna uku.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu