Isa ga babban shafi
Nigeria-Egypt

Matar Sanata Yerima na Masar.

Offishin Jakadancin kasar Masar dake Nigeria, yace yarinyar nan da ake zancen tsohon Gwamnan Jihar Zamfara ya aure ta, tana kasar Masar bata je Najeriya ba.  A tattaunawa da yayi da wasu kafofin yada labarai Tsohon Gwamna Ahmed Sani Yeriman Bakura, yayi ta musanta cewa ba karamar yarinya ya aura ba.Jakadan kasar Masar a Nigeria, Mohammed Saber ya fadi cewa yarinyar da ake zance na can kasar Masar tana karatu a Makaranta, kuma babu wanda ya kawo kara Offishin.Sai dai kuma yace Offishin Jakadancin zai bi diddigin wannan lamari, domin ganin cewa baa saba kaida ba wajen aurar da yarinyar.A jiya Majalisar Dattawan kasar ta bada umarnin gudanar da cikakken bincike gameda lamarin.Kungiyoyin mata a Najeriya dai nata barazanar sanya kafar wando daya da tsohon Gwamnan, saboda abinda suka kira « sauya matan aure da yakeyi tamkar yana sauya takalma » 

rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.