Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya ta karbi rigakafin Covid-19 miliyan 4 karkashin shirin Covax

Kusan alluran rigakafin Coronavirus miliyan 4 ne suka isa Najeriya yau Talata karkashin shirin Covax wanda hukumar Lafiya ta Duniya ke jagoranci da zai saukaka wadata matalautan kasashe da rigakafin.

Najeriya ta zama kasa ta 3 da ta karbi alluran rigakafin Coronavirus karkashin shirin na Covax.
Najeriya ta zama kasa ta 3 da ta karbi alluran rigakafin Coronavirus karkashin shirin na Covax. SIA KAMBOU AFP
Talla

Najeriyar mafi yawan jama’a a Nahiyar Afrika ta zama kasa ta 3 da ta karbi alluran rigakafin karkashin Covax bayan Ghana da Ivory Coast, a wani yunkuri na dakile yaduwar cutar da ke ci gaba da kisa a sassan Duniya.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito cewa jirgin Emirates dauke da alluran ya isa filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke babbar birnin Najeriyar Abuja tun da safiyar yau makare da alluran miliyan 3 da dubu dari 9 da 4 samfurin na hadakar jami’ar Oxford da AstraZenica amma wanda aka sarrafa a India.

Mabanbantan sanarwa da gwamnatin Najeriya da kuma Majalisar Dinkin Duniya suka fitar ta tabbatar da isar alluran Abuja, inda suka ce alluran wani bangare ne na allurai miliyan 16 da shirin na Covax ya alkawartawa Najeriya nan da watanni masu yawa don fara yiwa al’ummarta miliyan 200, bayan da cutar ta kashe mutane fiye da dubu dubu 1 da 915.

Sanarwar da Faisal Shu’aib shugaban kula da lafiya a matakin farko na Najeriya ya fitar ta ce jami’ansu sun shirya tsaf don fara alluran rigakafin akan jami’an Lafiya gabanin fadada shi zuwa daidaikun.

A watan da ya gabata ne hukumar kula da inganci abinci da magunguna ta Najeriya, NAFDAC ta amince da sahihancin nau’in maganin na AstraZeneca.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.