Isa ga babban shafi

An sauya wa wanda ake zargi da kisan dan takaran shugaban Ecuador gidan yari

Dubban yan sanda da sojoji ne a jiya Asabar suka halarci sauya wa wani kasurgumin  shugaban yan tsageran kasar Equateur, da aka zarga da yi  wa dan takarar shugabancin kasar Fernando Villavicencio  barazanar kisa, kwanaki 3 kafin kashe shi, kamar yadda mahukumtan kasar suka sanar.

Taswirar kasar Ecuador
Taswirar kasar Ecuador Wikimedia/Shadowfox
Talla

Matar marigayi M  Villavicencio, Veronica Suauz,  ta ce alhakin kisan mijin nata, da na kan kasar ne, tare da zargin magoya bayan tsohon shugaban kasar ta Equado Rafael Correa, da ke zaman gudun hijira a kasar Beljium, da zama umal’aba’isan aikata kisan, kai tsaye ko kuma ta hanyar wasu.

Akalla sojoji da yan sanda dubu 4000 ne, dauke da manyan makamai masu tarin yawa ne aka nuna cikin motoci masu sulke, a cibiyar kurkuku mai lamba takwas,  dake birnin Guayaquil, kudu maso yammacin kasar,  inda ake tsare da shugaban kakkarafar kungiyar yan tsageran Los Choneros, Mr Adolfo Fito Macias.

 

Hotunan da jami’an tsaro suka yada, sun nuna shugaban yan tsageran da gashi mai yawa ya lulluben kansa  hade da  kasumba, daure da sarka, yana samun rakiyar  jami’an tsaro, da kuma  wasu gwamman fursunonin da aka kwantar a kasa  ba sutura a jikinsu, daga su sai  kamfe.

Shugaban kasar ta Equado Guillermo Lasso, ya bayyana cewa, an sauya wa  Fito kurkuku  a Roca, kurkukun da aka tanadar wa kwararan matakan tsaro, inda ake kunshe da fursunoni 150, da ke wani bangare na gidan yarin na Guayaquil.

Tun bayan mutuwar Fernando Villavicencio ta hanyar harbin bindiga, sunan Fito, ya yi tambari a cikn kafofin yada labaran kasar Equado. Dan takarar mai shekaru 59 a duniya,  kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta      nuna cewa,  shi ne na biyu a farin jini  ga zaben shugabancin kasar da ake shirin gudanarwa a ranar 20 ga watan Ogustan 2023.

 

Yan kasar Colombia shida ne aka kama a lokacin harin, a yayin da aka kashe na  bakwan su a musayar wutar da ta hada su  da masu tsaron lafiyar dan takarar.

A makon da ya gabata, dan siyasar da aka kashe, ya bayyana cewa,  shugaban yan tsageran da aka zartarwa hukumcin daurin zaman gidan yari na shekaru 34, saboda aikata laifukan kisan kai da kuma safarar  miyagun kwayoyi ya yi masa barazanar kisa.

Marigayi Villavicencion, tsohon dan jarida ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.