Isa ga babban shafi
Mauritania

Shugaban Mauritania zai sake komawa Faransa don cigaba da neman magani

A yau Shugaban kasar Mauritania Mohamed Ould Abdel Aziz zai sake komawa birnin Paris a kasar Faransa, don ci gaba da duba lafiyar shi, kasa da mako daya da komawar shi gida, bayan da aka mishi magani sakamakon harbin shi da wani sojan kasar ya yi a watan da ya gabata.

Shugaban kasar Mauritania, Ould Abdel Aziz
Shugaban kasar Mauritania, Ould Abdel Aziz REUTERS/Darrin Zammit Lupi (
Talla

A jiya da dare shugaba Abdel Aziz, mai shekaru 55, ya shaidawa wani taron manema labarai cewa, dama ya shirya gani likitan a Faransa.
 

A ranar Laraba jama’iyyun adawan kasar suka kauracewa bukin cika shekaru 52 da samun ‘yancin kan Mauritania, don nuna adawa da mulkin shugaba Abdel Aziz.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.