Isa ga babban shafi
Girka

Majalisar Dinkin Duniya Ta Nemi Girka Tayi Takatsantsan

Ministan Kulada shige da fice na kasar Girka Christos Papoutsis ya kare matakan da kasar ta dauka na tsaurara matakan tsaro kan iyakokin kasar da  Turkiyya, inda yake cewa sunyi haka ne domin kare bakin haure marasa izini.Ita dai kasar Girka ta tsara killace yankin kasar ta mai tsawon kilomita 12 da waya.Kwamishinan Kula da ‘Yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya ya yi  kira ga Hukumomin kasar Girka suga lallai matakin su na yaki da bakin haure bai muzgunawa masu neman mafaka ba  daga kasashen Afghanistan, Iraki da Somalia.Kwamishinan wadda take kula da shige da fice na Turai Cecilia Malmstroem tace ‘yan gudun hijra dake zuwa Girka na cikin wani hali.Mai magana da yawun ta Michele Cercone yace matakan killace kan iyakoki da wayoyi ko kuma gini, zai kasance  mataki ne na dan wani lokaci.Bayanai na nuna cewa daga watan Janairu na bara zuwa watan Nuwamba data gabata bakin haure da suka shiga kasar Girka ba tare da izini ba sun kai 32,500  wadan da  aka kama su.Ma'aikatan tsaron kan iyakokin  kasar da aka diba sun kai 200 da niyyar hana yawan masu zuwa kasar cin arziki. 

Jami'an tsaro dake gadin kan iyakan kasar Girka da Turkiyya.
Jami'an tsaro dake gadin kan iyakan kasar Girka da Turkiyya. rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.