Isa ga babban shafi

Kungiyar mayakan Hamas ta bayyana cewa harin Isara'ila ya yi muni a Gaza

Kungiyar Hamas mai gwagwarmaya da makamai a Falatsinu  na duban wani shirin tsagaita wuta a Gaza yayin da yakin da suke gwabzawa da Isra'ila ya doshi watani  5.

Harin da Isra'ila ta kaiwa Faledinu a  Jabalya yanzkin zirin Gaza.
Harin da Isra'ila ta kaiwa Faledinu a Jabalya yanzkin zirin Gaza. REUTERS/Suhaib Salem
Talla

Mummunan farmakin da Isra'ila ta kai a zirin Gaza ya yi sanadin mutuwar mutane da dama a daren jiya Lahadi a daidai lokacin da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ke auna sabuwar shawarar tsagaita  wuta domin dakatar da yakin da aka kwashe watanni hudu ana gwabzawa.

Babban jami'in diflomasiyyar Faransa  ya fara ziyararsa ta farko a yankin Gabas ta Tsakiya , da nufin sa kaimi ga tsagaita  wuta da kuma makomar wadanda akayi garkuwa da su, , kuma ana sa ran sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken zai  kai ziyara yankin.

Ma'aikatar lafiya ta Gaza ta ce hare-haren da Isra'ila ta kai cikin dare sun kashe akalla mutane 92.

Isra'ila ta yi gargadin cewa dakarunta na kasa za su iya tunkarar Rafah, inda dubban mutanen da ke neman mafaka daga matsugunin a wani sansani na wucin gadi.

Amma wani babban jami'in Hamas a Lebanon, Osama Hamdan, ya bayyana cewa shirin  da aka tsara domin tsagaita wuta bai cika wasu sharuda ba.

Yakin dai ya samo asali ne sakamakon kutsen da Hamas ta yi a Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba yayin da mutane kusan 1,160, galibi fararen hula suka rasa rayukansu.

 A martanin da Isra'ila ta mayar, ta kaddamar da wani farmakin da ya kashe akalla mutane  27,365 a Gaza, galibi mata da kananan yara,

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.