Dakarun Isra’ila sun kama darakta asibitin Gaza na Al-Shifa
Wani likita a babban asibitin Gaza Al-Shifa ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa dakarun Isra'ila sun kama daraktan cibiyar da wasu ma'aikatan lafiya da dama a yau Alhamis.
Wallafawa ranar:
Daraktan asibitin mai suna Mohammad Abu Salmiya na daya daga cikin mutanen da Isra;ial ke kalo a matsayin Wanda ke sanar da Duniya halin da ake ciki a duk lokacin da aka samu mutanen da suka jikkata ko suka mutu biyo vayan harin dakarun Isra’ila yankin na Gaza.
A daya gefen sojojin Isra'ila da suka kai samame asibitin a makon da ya gabata, sun yi zargin cewa mayakan Hamas sun yi amfani da wani rami da ke karkashin cibiyar a birnin Gaza wajen kai hare-hare.
Zargin da kungiyar Hamas da jami'an asibiti suka sha musantawa.
Khalid Abu Samra, shugaban sashen asibitin ya sheidawa manem alabarai cewa ‘’an kama Dakta Mohammad Abu Salmiya tare da wasu manyan likitoci,"kuma nan take kungiyar ta Hamas ta yi Allah-wadai da kamun da aka yi ma’aikatan asibitin, tana mai kira ga kungiyar agaji ta Red Cross da sauran kungiyoyin kasa da kasa da su yi kokarin ganin an sako su cikin gaggawa.
A ranar Asabar da ta gabata ne ,dakarun Isra’ila suka bayar da umarnin ficewa daga asibitin , lamarin da ya sa daruruwan majinyata ke gudun hijira tare da yin kaura zuwa kudancin Falasdinu.
Domin wanke kansu daga duk wani zargin cin zarrafi,dakarun Isra’ila sun fitar da wani faifan murya ,wanda ke tabbatar da zargin da Isra'ila ke yi cewa Hamas na gudanar da wata cibiyar ba da umurni a cikin ramukan da ke ƙarƙashin asibitin na tsawon shekaru - zargin da ƙungiyoyin Hamas da ma'aikatan lafiya suka fatali da shi.
A ranar Laraba, sojojin Isra'ila sun raka 'yan jarida zuwa daya daga cikin ramin da suka ce wani bangare ne na wata babbar hanyar sadarwa ta karkashin kasa da Hamas ke amfani da shi.
Asibitin Al-Shifa dai ya kasance wurin da dakarun Isra'ila suka kara kai farmaki a wani bangare na yakin da suke yi da kungiyar Hamas a zirin Gaza, inda gwamnatin Hamas ta ce an kashe fiye da mutane 14,000 wadanda yawancinsu mata da yara ne.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu