Isa ga babban shafi

Akalla ‘yan jarida 42 ne aka kashe tun fara yakin Gaza - CPJ

Binciken farko da kwamitin kula da ‘yan jarida na kasa da kasa CPJ ya gudanar ya nuna cewa akalla ‘yan jarida 42 da ma’aikatan yada labarai ne aka kashe tun bayan fara yakin Isra’ila da Hamas a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda  ke zama mafi muni ga ‘yan jarida tun bayan fara tattara bayanan CPJ a shekarar 1992.

Jana'izar dan jaridar Faladinawa Mohammed Abu Hatab a yankin Gaza.3/11/23
Jana'izar dan jaridar Faladinawa Mohammed Abu Hatab a yankin Gaza.3/11/23 AFP - MAHMUD HAMS
Talla

Cikin sanarwa da kungiyar ta fitar, ta nuna cewa; ya zuwa ranar Litinin, “an tabbatar da mutuwar ‘yan jarida 42 da ma’aikatan yada labarai, cikin harda Falasdinawa 37, da ‘yan Isra’ila hudu, da kuma dan Lebanon daya.

CPJ tace ‘yan jarida tara sun jikkata, yayin da aka ruwaito bacewar 'yan jarida uku, sannan an kama ‘yan jarida 13.

Shugaban kwamitin na CPJ mai kula da Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka Sherif Mansour y ace ‘Yan jarida ke aiki a yankin na cikin mawuyacin hali.

'Yan jaridar da ke tattara labarai a yaƙin sun kuma fuskanci "hari da barazana da hare-hare ta yanar gizo, da kuma kashe 'yan uwasu"

.Jami’in ya kara da cewa 'Yan jarida na sadaukarwa sosai domin fayyacewa al'umma halin da ake ciki a yankin da ke gudana a yankin Gabas ta Tsakiya.

"Yan jarida a fadin yankin na sadaukarwa sosai don sanin halin da ake cikin a wannan rikici mai ratsa zuciya,"

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.