Isa ga babban shafi

Isra'ila na ci gaba da zafafa hare-hare a Zirin Gaza

Isra’ila ta ci gaba da luguden wuta a kan yankin Zirin Gaza a cikin daren jiya Lahadi zuwa safiyar Litinin din nan, inda yanzu haka ma’aikatar lafiyar Hamas ke cewa Falasdinawa 400 ne suka mutu a cikin sa’o’i 24 da suka gabata. 

Prime ministan Isra'ila Benjamin Natenyahu
Prime ministan Isra'ila Benjamin Natenyahu © ABIR SULTAN/REUTERS - POOL
Talla

Isra’ilar ta yi ruwan wuta a kan yankunan da ke kunshe da gidajen jama’a, da suka hada da asibitocin Al-Shifa da Al-Quds, da kuma sansanin ‘yan gudun hijirar nan na Jabalia, inda ‘yan gudun hijira 20 suka mutu, gwammai suka jikkata. 

Rahotanni sun tabbatar da cewa a yankin Rafah, hare-haren na Isra’ila sun wargaje dogayen benaye 5 da jama’a ke zaune a ciki, inda hukumar kwana-kwana ta ce mutane 50 sun mutu a cikin wadannan gine-gine. 

Akalla mutum guda ya mutu, 5 kuma suka samu munanan raunuka bayan da dakarun Isra’ila suka suka bude wuta a wasu jerin samame da suka kai yankin yammacin kogin Jordan. 

Ma’aikatar lafiyar yankin Falasdinu ta ce dakarun na Isra’ila sun bude wutar ne  a yayin da suka kai samame sansannin ‘yan gudun hijira na Jalazounn a arewacin birnin Ramallah, kuma sun yi wa dimbim mutane kofar raggo a Ramallah da Nablus. 

Mahukuntan asibitin Al-Aqsa sun ce kaso 65 na wadanda aka kai asibitin a cikin daren jiya Lahadi yara ne kanana. 

A waje daya kuma, sojin Isra’ila ta ce ta kai hari kan sansanonin kungiyar Hezbollah a Lebanon a safiyar Litinin din nan, tana maiikirarin cewa su na shirinkai mata farmaaki da rokoki daa makami masu linzami. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.