Mutane 2 sun mutu a wani harin da aka kai ofishin jakadancin Amurka a Saudiya
Mutane 2 da suka hada da wani mahari sun mutu a cikin wata musayar wuta da ta faru a jiya Laraba a gaban karamin ofishin jakadancin Amurka dake birnin Jiddah na Saudiyya, kamar yadda mahukuntan masarautar suka sanar.
Wallafawa ranar:
KamfanindillancinlabaranSaudiya SPA ya sanar da cewaMutumindakedauke da bindiga ya saukane daga cikinmotarsa a gabangininkafin a kasheshi a cikinwatamusayarwuta da jami’antsaro.
A cewarkakakinyansanda, wanijami’intsarodaya, dan asalinkasarNepal ya mutusakamakonraunin da ya samu.
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce babu wani dan kasarta da ya jikkata a ofishin jakadancinta, wanda aka takaita zirga-zirga a kewayensa.
A wata sanarwa, ma’aikatar ta mika sakon ta’aziyarta ga iyalan mai gadin da ya mutu a harin, inda ta ce tana tattaunawa da masarautar Saudiyyar, wadda ta kaddamar da bincike a kan lamarin.
Wannan harin na zuwa ne daidai lokacin da Saudiyya ke karbar bakunci masu aikin hajji kusan miliyan biyu daga sassan duniya da ke sauke farali a birnin Makka, kilomita kusan 70 daga ofishin jakadancin Amurka.
Ofishin jakadancin Amurka ya fuskanci hare-hare a lokuta dabam dabam a shekarun baya, inda a ranar 4 ga watan Yuli ta shekarar 2016, wato ranar bikin samun yancin kan Amurka, wani dan kunar bakin wake ya tarwatse kansa a ofishin.
A watan Disamban shekarar 2004, wani hari ya yi sanadin mutuwar mutane 5 a ofishin jakadancin na Amurka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu