Isa ga babban shafi

Salman ya kai ziyarar farko Turkiya bayan kisan da aka yi wa Kashoggi

Yarima mai jiran gadon Sarautar Saudiya ya kai ziyara ta farko zuwa Turkiya, tun bayan kisan gillar da aka yi wa dan jarida Jamal Kashoggi a cikin ofishin jakadancin kasarsa Saudiya dake birnin Santambul.

Shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan yayin karbar bakuncin Yarima mai jiran gadon sarautar Saudiya Muhammad bin Salman.
Shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan yayin karbar bakuncin Yarima mai jiran gadon sarautar Saudiya Muhammad bin Salman. © Présidence turque - AP
Talla

Ganawa tsakanin Yarima Muhammad bin Salman da shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan ta zo ne wata guda kafin ziyarar da shugaban Amurka Joe Biden ke shirin kaiwa zuwa birnin Riyadh na Saudiya, domin halartar taron da zai mayar da hankali kan matsalar karanci da kuma hauhawar makamashin da ya kunshi iskar gas da man fetur, saboda yakin Rasha da Ukraine.

Masu sharhi na ganin cewar, batutuwan tattalin arziki da kuma huldar kasuwanci na daga cikin manyan dalilan da suka sanya yarima mai jiran gadon sarautar Saudiya daukar matakin gyara alakar dake tsakaninsa da daya daga cikin kasashe na gaba gaba masu adawa da shi.

Erdogan na fuskantar kalubalen daidaita tattalin arzikin Turkiya

Yanzu haka dai tattalin arzikin kasar Turkiya na fuskantar koma baya, yayin da ya rage shekara guda babban zaben kasar ya gudana, kalubalen dake zama barazana ga gwamnatinsa da ya shafe shekaru 20 yana jagoranta.

Gwamnatin shugaba Erdogan ce dai ta wallafa rahoton binciken da ya fayyace yadda aka aiwatar da mummunan kisan gillar da aka yi wa marigayi Kashoggi, ciki har da zargin da ake na yi wa gawarsa gunduwa gunduwa tare da narkar da ita a cikin ruwan acid.

Sai dai a yanzu shugaba Erdogan na kokarin janyo hankalin masu zuba hanun jari da kuma neman taimakon kasashen Larabawan da a baya yake adawa da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.