Isa ga babban shafi
Sauyin Yanayi

Guguwar yashi ta kwantar da mutane dubu 2 a asibiti

Wata kakkarfar guguwar yashi ta sake barkewa ranar litinin a Iraqi, lamarin da ya tilasta garzayawa da mutane akalla dubu 2 zuwa asibiti saboda sarkewar numfashi, sai kuma rufe tashoshin jiragen sama, da makarantu, da kuma hukumomin gwamnati a fadin kasar.

Guguwar ta karade wurare da dama a Iraqi
Guguwar ta karade wurare da dama a Iraqi Reuters/Bassam Khabieh
Talla

Wannan dai shi ne karo na takwas da kakkarfar guguwar yashin da ke turnuke sararin samaniyar yankunan Iraqi da dama ke afka wa kasar, tun daga tsakiyar watan Afrilu zuwa wannan lokaci.

Kasar ta Iraqi na fuskantar wannan iftila’i ne a daidai lokacin da take fama da tsanantar matsalolin da suka hada da fari, lalacewar kasar noma, da karancin ruwan sama wadanda kwararru suka alakanta da sauyin yanayi.

Guguwar yashi ta karshe da ta afkawa sassan Iraqi a farkon wannan watan sai da tayi sanadin mutuwar mutum guda, yayin da aka kwantar da wasu mutanen akalla dubu 5,000 a asibitoci, saboda matsalar numfashi.

Wakilan kamfanin dillancin labarai na AFP sun ruwaito cewar, a litinin din nan, ‘yan Iraqi suka wayi gari da ganin kura mai kaurin gaske mai jan launi da ta lullube birnin Bagadaza tare da lullube wasu garuruwa da dama da suka hada da birnin Najaf da kuma Sulaimaniyah da ke yankin arewacin Kurdawa mai cin gashin kansa.

Bayanai sun ce, guguwar ta sanya kakkauran yashin rufe rufin gine-gine da motoci, har ma da kutsawa cikin gidaje, tare da rage karfin nisan ganin idanu zuwa mitoci 300 kacal a filin jirgin saman Bagadaza, lamarin da ya tilasta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.