Isa ga babban shafi

Falasdinawa na gangamin tunawa da ranar 'Nakba'

Falasdinawa na gangamin zagayowar ranar da suka yi wa Lakabi da “Nakba” wadda a cikinta suke tunawa da lokacin da Isra’ila ta mamaye yankin Falasdinu a ranar 15 ga Mayu, na shekarar 1948.

Wasu Falasdinawa a yayin gangamin tunawa da ranar 'Nakba' da Isra'ila ta fara mamaye yankunansu.
Wasu Falasdinawa a yayin gangamin tunawa da ranar 'Nakba' da Isra'ila ta fara mamaye yankunansu. Anadolu Agency via Getty Images - Anadolu Agency
Talla

A rana mai kamar irin ta Lahadin nan,  aka kafa Isra’ila a matsayin kasa, lamarin da yayi sanadin rabuwar Falasdinawa fiye da dubu 700 da muhallansu a tsakanin shekarun 1947 zuwa 1949.

Wasu bayanai daga kungiyoyin fafutukar kare yankin Falasdinu sun ce a waccan lokaci Isra’ila sun tayar da kauyukan Falasdinawa fiye da 500 a yayin da dubbai daga cikinsu suka rasa rayukansu.

Bikin zagayowar ranar Nakba ta bana da ke cika shekaru 74 ya zo ne a daidai lokacin da mutane da dama ke bayyana bacin ransu kan kisan gillar da aka yi wa fitacciyar ‘yar jaridar Aljazeera Shireen Abu Akleh, yayin da take daukar rahoto a gabar yamma da kogin Jordan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.