Isa ga babban shafi
Iran

Jami'an tsaron Iran sun zafke mutane 67 yayin zanga-zanga a Isfahan

Gwamnatin Iran ta tura ‘yan sandan kwantar da tarzoma zuwa birnin Isfahan, kwana guda bayan da aka kama mutane da dama daga cikin masu zanga-zangar nuna bacin rai kan karancin ruwan sha da na noman rani.

Mazauna garin Isfahan yayin zanga-zangar adawa da bushewar Kogin Zayandhrod. Ranar 19 ga Nuwamba, 2021.
Mazauna garin Isfahan yayin zanga-zangar adawa da bushewar Kogin Zayandhrod. Ranar 19 ga Nuwamba, 2021. © Fatmeh Nasr / ISNA / AFP
Talla

Bayanai sun ce jami’an tsaron sun harba barkonon tsohuwa yayin arangama da masu zanga-zangar da suka rika jifansu da duwatsu a gaf da kogin Zayadneh Rood da ya ratsa birnin na Isfahan, kogin da a yanzu ke ja da baya, wanda ke da muhimmanci ga manoma da sauran jama’ar gari.

Mai Magana da yawun ‘yan sandan Iran Janar Hassan Karami ya ce kawo mutane 67 suka cafke daga cikin wadanda suka gudanar da zanga-zangar, da ya ce akalla mutane dubu 2 zuwa 3 ne suka sami halartarta.

A makon da ya gabata dai kimanin manoma da sauran jama’ar gari dubu 30,000 zuwa dubu 40,000 ne suka halarci zanga-zangar bayyana bacin ran kan karancin ruwan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.