Isa ga babban shafi

‘Yan bindiga sun kashe mutane 11 a Baluchistan dake Pakistan

‘Yan bindiga rabin dozin sun kashe mutane 11 a yammacin ranar Juma’a, ciki har da ma’aikatan Punjabi tara a Baluchistan, lardin da ke kudu maso yammacin Pakistan da ke fama da tashe-tashen hankula akai-akai, in ji hukumomin yankin.

Jami'an tsaro na kasar Pakistan
Jami'an tsaro na kasar Pakistan AP - Fareed Khan
Talla

Rahotanni daga yankin na nuni cewa wasu mutane shida dauke da makamai sun tsayar da wata motar bas a kusa da garin Naushki da yamma, inda suka duba takardun mutanen da ke ciki sannan suka tafi da ma'aikatan Punjabi guda tara, 'yan kabilar da ke da rinjaye a Pakistan.

Yan lokuta vayan awon gab da su, an kuma gano gawarwakinsu, kilomita biyu daga babbar hanyar. Wani jami'in 'yan sandan yankin Allah Bakhsh ya shaida wa AFP cewa "Sun harbe su yan lokuta vayan ficewa da su."

Yankin Sohbat Pur, a  Balouchistan, na kasar Pakistan
Yankin Sohbat Pur, a Balouchistan, na kasar Pakistan AP - Zahid Hussain

Maharan suka yi harbin kan motar mataimakin lardin, biyu daga cikin mutanen sun mutu bayan da motar ta fada cikin rami.

Habibullah Musakhail, wani babban jami'in yankin ya ce "'Yan sanda da jami'an tsaro sun yi artabu da wurin domin kamo maharan, amma tuni suka gudu."

Har ya zuwa safiyar yau Asabar ba a kai dauki ba, amma Allah Bakhsh, babban jami’in ‘yan sandan yankin ya ce harin na dauke da alamar ‘yan awaren Baluchistan.

Yan Sanda a kasar Pakistan
Yan Sanda a kasar Pakistan AP - Fareed Khan

Shekaru da dama, wannan lardi mai fadi, matalauta da marasa galihu, ya sha fama da tashe-tashen hankula na kabilanci, na bangaranci da na 'yan aware.

Kasar Balochistan dai na da arzikin samar da iskar gas da ma'adanai, amma al'ummarta na korafin yadda ake warewa tare da sace albarkatun kasa.

'Yan tawayen a kai a kai suna kai hari a Punjabis da Sindhis da ma'aikatan kamfanonin kasashen waje da ke aiki a bangaren makamashi.

Yankin Sistan-Balouchistan,a Zahedan.
Yankin Sistan-Balouchistan,a Zahedan. AFP

Sai dai jami'an tsaron Pakistan ne suka fi fuskantar hare-haren 'yan awaren da ke cewa al'ummarsu ne ake yi wa kisan gilla da kuma yin garkuwa da su.

Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif ya bayyana harin na daren Juma'a a matsayin "na ta'addanci" a cikin wata sanarwa da ya ce " bincike na tafiya a kai kuma za a hukunta su."

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.