Isa ga babban shafi

Saudiyya ta ce ba a ga jinjirin watan Shawwal ba

Kotun Kolin Saudiyya ta ayyana Talata a matsayin ranar da watan Ramadan zai cika kwanaki 30, abin da ke nufin cewa, za a gudanar da bikin Karamar Sallah a ranar Laraba da ke matsayin 1 ga watan Shawwal.

Wasu masu duban jinjirin wata
Wasu masu duban jinjirin wata © Achmad Ibrahim / AP
Talla

Kotun ta fitar da sanarwar ce bayan Kwamitin Duban Wata na Kasar ya ce, bai ga jinjirin wata ba a Litinin din nan da ke zama 29 ga watan Ramadan, a don haka za a cika azumin bana zuwa kwanaki 30.

Da ma dai ganin jinjirin watan shi ke nuna farawa ko kuma kammala azumin Ramadan kuma galibi, kasashen Musulmai sun fi gudanar da azumi 29 a maimakon 30.

Sai dai a bana, masana kimiya sun danganta rashin ganin jinjirin watan na Shawwal da kusufin rana da aka samu a kasashen yankin Amurka a Litinin din nan, wanda ya haddasa ɓuyar jinjirin watan a yammacin nan.

A cewar masana kimiya ana samun kusufin ne a sakamakon yadda wata ke shiga tsakanin hanyar rana da wannan doran kasan da muke rayuwa a kansa, yayin da a bana aka samu kimanin mintina 5 na ganin duhun da kusufin ya haddasa da ranar tsaka a wadannan kasashe.

Sanarwar da mahukuntan Saudiyya suka fitar ta bukaci al'ummar Musulmai da su yi amfani da sauran sa'o'in da suka rage a cikin watan na Ramadan wajen ci gaba da gudanar da ibada da kuma ayyuka na alheri.

Kazalika sanarwar ta yi fatan Allah Ya tsawaita rayukan Musulmai  cikin koshin lafiya domin ci gaba da azumtar Ramadan a shekaru masu yawa nan gaba.

Sauran kasashen da su ma suka ce ba su ga jinjirin watan na Shawwal ba sun haɗa da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Oman da Qatar da Kuwait da Bahrain da Masar da Turkiya da Iran da wasu tarin kasashe a yankin Gabas ta Tsakiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.