Isa ga babban shafi

Ɗan Birtaniya ya kafa tarihin karaɗe nahiyar Afrika da gudu

Wani Baturen Birtaniya da ya kira kansa " jarumin namiji" ya kammala gudun karaɗe nahiyar Afrika cikin wani gagarumin kalubale a kasa da shekara guda.

Russ Cook da ya kammala tseren kewaye daukacin Afrika
Russ Cook da ya kammala tseren kewaye daukacin Afrika REUTERS - Zoubeir Souissi
Talla

 

Russ Cook, dan asalin Worthing da ke Yammacin Sussex a Birtaniya, ya samu gagarumar tarba daga masoyansa a lokacin da ya kai iyakar karshe da ke alamta kammala sassarfarsa a Ras Angela da ke kasar Tunisia wadda ke can yankin arewacin Afrika a ranar Lahadin da ta gabata. 

Abin ya yi kyau, na gaji. Inji Cook

Ya fara gudun ne na tsawon kilomita dubu 16 daga yankin Kudancin Cape Agulhas da ke Afrika ta Kudu a ranar 2 ga watan Afrilun 2023.

Gabanin kammala balaguronsa mai cike da kalubale, matashin mai shekaru 27 ya bayyana cewa, zai kafa tarihin zama mutun na farko da ya yi gudun karaɗe tsawon nahiyar Afrika.

Wasu daga cikin magoya bayansa da suka taya shi murnar kammala gudun.
Wasu daga cikin magoya bayansa da suka taya shi murnar kammala gudun. REUTERS - Zoubeir Souissi

Ya tsallaka ta kan iyakokin kasashen Afrika 16, sannan ya yi tseren nisan kwatankwacin gudun-yada-kanin-wani har guda 376.

Daya daga cikin magoya bayansa wanda ya taya Mista Cook gudun wata ƴar tazara ya ce, 

Na fahimci matata na da juna biyu, har ta kuma haihu, yanzu muna da jariri wanda ya cika watanni biyu da haihuwa a daidai lokacin da (Cook) ya kammala tseren. Wannan zai taimaka wajen kiyaye tarihin da ya kafa.

Ƴan sa'o'i gabanin kammala tseren, Mista Cook ya wallafa wani sako a shafinsa na X, inda yake cewa " Abin kamar al'amara, na kusan kammalawa. Ina dakon ku a garejin Shell nan kusa, ya ku maza da mata".

Kalubalen da Mista Cook ya fuskanta a kasashen Afrika

Mista Cook wanda ya samar da sama da Pam dubu 600 ga gidauniyar sadaka, ya fuskanci kalubalen tsananin zafi da gajiyar gabobi da ya yi juriya a kai.

A kasar Angola, ƴan fashi da makami sun tare shi da tawagarsa, inda suka karbe musu kyamarori da wayoyin salula da takardun fasfo.

Kazalika a cikin watan Agusta, Mista Cook ya yi batan-dabo, inda har tawagar magoya bayansa ta gaza nemo sa a tsawon kwanaki a cikin wani gandun dajin da ke Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo.

Daga bisani an karbo shi daga hannun wasu mazauna karkara masu dauke da makamai da adduna bayan an biya kudin fansa.

Algeria ta taimaka wa Cook da bisa na musamman

A cikin watan Janairu, ya yi amfani da kafar sadarwa ta zamani wajen neman taimakon samun takardun bisa domin samun izinin tsallaka kan iyakar Mauritania zuwa Algeria.

A wancan lokacin, Mista Cook ya ce, akwai yiwuwar ya katse wannan tseren nasa sakamakon rashin samun bisar, amma daga bisani Ofishin Jakadancin Algeria ya ce, lallai zai samar masa da bisa ta musamman nan take.

Magoya bayansa sun taya shi kammala gudunsa a rana ta karshe.
Magoya bayansa sun taya shi kammala gudunsa a rana ta karshe. REUTERS - Zoubeir Souissi

A rana ta karshe ta kammala gudun nasa, Mista Cook ya gayyaci magoya bayansa da su taya shi kammala gudun tazarar da ta rage masa, yayin da ya sanar da shirya gagarumin biki a otel din Bizerte da ke Tunisia domin murnar kammala gudun lami-lafiya.

Ba a karon farko kenan da Cook ke yin irin wannan balaguron ba, domin ko a lokacin da yake dan shekara 22, ya yi tsere daga nahiyar Asiya zuwa Ingila, inda ya kammala gudun-yada-kanin-wani 71 cikin kwanaki 66.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.