Isa ga babban shafi

Isra'ila ta kori kafar talibijin ta Al Jazeera

Majalisar dokokin Isra'ila ta kada kuri'ar amincewa da korar kafar talibijin ta Al Jazeera daga cikin kasar, sakamakon abin da ta kira kare muradun kasar, musamman sha'anin tsaro.

Tambarin gidan yada labarai na Aljazeera
Tambarin gidan yada labarai na Aljazeera bloviatingzeppelin.net
Talla

Wannan na zuwa ne, bayan da ministan yada labaran kasar, Shlomo Karhi ya sanar da cewa nan da 'yan kwanaki za a rufe duk wani ofishin Al Jazeera da ke cikin kasar.

Tuni dai Firaminista, Benjamin Netanyahu ya yi maraba da matakin majalisar dokokin kasar, yana mai cewa, lokaci ya yi da ya kamata Al Jazeera ta daina daukar labarai daga Isra'ila.

Gidan talibijin din mai shalkwata a birnin Doha na kasar Qatar, ya bayyana cewa, tun da farko an yi barazanar yin amfani da matakan gaggawa don murkushe ofisoshin Al Jazeera a Isra'ila da yankunan Falasdinawa da aka mamaye.

A tsakiyar watan Oktoba, gwamnatin Isra'ila ta zartar da manufofin da za su bata damar rufe kafafen yada labaran kasashen waje na wani dan lokaci, yayin da take musu kallon barazana ga muradun kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.