Isa ga babban shafi

Fafaroma Francis ya bukaci samar da zaman lafiya a ƙasashe da ke cikin yaƙi

Shugaban mabiya mazahabar ɗarikar Katolika ta duniya, Fafaroma Francis ya bukaci al’ummar duniya su kauce wa hikimar amfani da makamai, su rungumi zaman lafiya da salama a saƙonsa na bikin Easter a ranar Lahadi.

Fafaroma Francis ya albarkaci taron jama'a yayin da yake jagorantar taron Easter a wani bangare na bukukuwan makon mai tsarki, a dandalin St Peter da ke fadar Vatican a ranar 31 ga Maris, 2024.
Fafaroma Francis ya albarkaci taron jama'a yayin da yake jagorantar taron Easter a wani bangare na bukukuwan makon mai tsarki, a dandalin St Peter da ke fadar Vatican a ranar 31 ga Maris, 2024. AFP - TIZIANA FABI
Talla

A jawabin da ya saba gabatarwa duk shekara, Farancis ya caccaki yaki, yana mai nuni da halin tashin hankali da ake ciki a Ukraine da Gaza da Sudan da Myanmar da sauran sassan duniya

Ya sabanta bukatar tsagaita wuta a Gaza, yana mai kira  a isar da kayan agaji ga yankin da yaƙi ya ɗaiɗaita, tare da sakin wadanda Hamas ta ke garkuwa da su, inda ya ce fararen hula sun kai maƙura wajen juriya, iyana mai kokawa da tasirin yakin a kan ƙananan yara.

Rasha - Ukraine

Fafaroman ya kuma yi tayin musanyar fursunoni tsakanin Rasha da Ukraine, a yayin da aka shiga shekara ta 3 a yaƙin da su ke gwabzawa.

Fafaroma Francis ya albarkaci taron jama'a yayin da yake jagorantar taron Easter a wani bangare na bukukuwan makon mai tsarki, a dandalin St Peter da ke fadar Vatican a ranar 31 ga Maris, 2024.
Fafaroma Francis ya albarkaci taron jama'a yayin da yake jagorantar taron Easter a wani bangare na bukukuwan makon mai tsarki, a dandalin St Peter da ke fadar Vatican a ranar 31 ga Maris, 2024. AFP - TIZIANA FABI

Sujadar sanya  albarka ga duniya da Fafaroman ma shekaru 87 ya gabatar a gaban mabiya dubu 60 da suka hallara a dandalin Saint Peter na birnin Vatican ya kawar da fargabar da ake a game da lafiyar jagoran na Katolika a duniya.

Ana bikin Easter ne dun tunawa da tashin Yesu Almasihi daga matattu, kuma shi ke alamta shiga  mako mai tsarki, wani lokaci mai tsarki a cikin kalandar mazahabar Katolika  mai mabiya biliyan 1 da miliyan dari 3 a fadin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.