Isa ga babban shafi

Kungiyar kasashen Larabawa ta bukaci gaggauta shigar da kayan agaji Gaza

Kungiyar kasashen Larabawa ta bukaci gaggauta tsagaita wuta a hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kaiwa yankin Gaza na Falasdinu, hare-haren da zuwa yanzu suka hallaka mutanen da yawansu ya haura dubu 31.

Fiye da kashi 2 bisa 3 na al'ummar Gaza ne yanzu haka ke cikin matsanancin halin bukatar agajin abinci da magunguna.
Fiye da kashi 2 bisa 3 na al'ummar Gaza ne yanzu haka ke cikin matsanancin halin bukatar agajin abinci da magunguna. © David Dee Delgado / Reuters
Talla

Yayin taron kungiyar karo na 161 da ya gudana a birnin Alqahira na Masar shugaban taron kuma wakilin Mauritania a kungiyar Hussein Sidi Abdellah Deh ya shaidawa zaman taron cewa wajibi ne a bayar da kariya ga tarin kananan yara da tsofaffin da yunwa ke ci gaba da tagayyarawa a Gaza.

Abdellah Deh ya koka da yadda Isra’ila ke daukar tsauraran matakan da ke hana jami’an agaji iya shigar da kayaki yankin na Gaza duk kuwa da tsananin bukatar agajin da al’ummar yankin ke da shi a yanzu.

Sanarwar bayan taron na birnin Alqahira ta ruwaito ilahirin shugabancin kungiyar na neman lallai dukkanin masu ruwa da tsaki su tabbatar da wadatuwar abinci da sauran kayakin bukata a yankin na Gaza baya ga dakatar da hare-haren Isra’ila a yankin.

Ko a makon jiya Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa kashi biyu bisa 3 na al’ummar Gaza na tsananin bukatar agajin abinci yayinda mutum miliyan 2 da dubu 300 ke cikin hadarin yunwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.