Isa ga babban shafi
Rasuwar Salissou Hamissou

Takaitaccen tarihin marigayi Salissou Hamissou

Allah Ya yi wa daya daga cikin ma'aikatan sashen Hausa na RFI, wato Muhammane Salissou Hamissou rasuwa sakamakon hatsarin mota a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya. 

Salissou Hamissou na gabatar da labaran karfe 5 agogon Najeriya da Nijar
Salissou Hamissou na gabatar da labaran karfe 5 agogon Najeriya da Nijar © RFI/ FMM
Talla

Bayanan da muka samu na cewa, hatsarin ya auku ne a cikin daren da ya gabata na Laraba wayewar Alhamis kuma nan ta ke Salissou ya koma ga mahaliccinsa.

'Yan uwa da abokan arziki sun shafe tsawon lokaci suna ta kokarin neman sa ta wayar salula, amma abin ya ci tura, lamarin da ya jefa hatta abokan aikinsa na RFI cikin firgici, yayin da muka fara gudanar da bincike don sanin halin da ya ke ciki.

Tuni aka dauki gawar Mahammane Salissou Hamissou zuwa birnin Maradi na Jamhuriyar Nijar, inda za a yi masa jana'iza a gobe Juma'a kamar yadda addinin Islama ya tanada.

Takaitaccen tarihin Salissou Hamissou

An haife shi ne a ranar 31 ga watan Agustan shekarar 1972 a birnin Yamai da ke Jamhuriyar Nijar kuma ya yi karatun addini da na boko a birnin.

Ya shafe sama da shekaru 30 yana aikin jarida, inda ya yi aiki da wasu kafafen yada labarai na cikin gida a Nijar kamar Amfani da R&M da kuma Tambara, gabanin tafiya sashen Hausa na Radio Iran.

Shi ne mutun na farko da ya fara karanta labaran duniya a sashen Hausa na RFI shekaru 17 da suka gabata, inda a wancan lokacin ya jagoranci labaran karfe 5 na yamma agogon Najeriya da Nijar.

Salissou Hamissou ya kasance a sahun farko na ma'aikatan da aka bude sashen Hausa na RFI da su a ranar 21 ga watan Mayun shekarar 2007.

Marigayin ne ke jagorantar shirin "Dandalin Nishadi" da ake watsawa a duk ranar Asabar tare da maimaicinsa a ranaar Lahadi na tsawon minti 20, duk da cewa yafi shahara da shirinsa na Al'adunmu na Gado.

Mahammane Salissou Hamissou ya kasance mutun mai barkwanci da kyakkyawar alaka tsakaninsa da ma'aikata da abokai da iyalansa.

Mutane da dama da ke sauraren Sashen Hausa na RFI daga sassan duniya na ci gaba da aiko da sakwannin ta'aziyar wannan babban rashin da aka yi.

Ya rasu ya bar 'ya'ya 6 da kuma mata guda, sai iyayensa biyu da ke raye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.