Shugaban kasar Iran ya isa kasar Saudiya domin halartar wani taro kan Gaza
Shugaban kasar Iran Ibrahim Raïssi ya isa Saudiya a yau Asabar domin halartar taron kasashen Larabawa da Musulunci kan yakin da ake yi tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas ta Falasdinu a zirin Gaza, kamar yadda kafar talabijin ta Al-Ekhbariya ta Saudiya ta sanar.
Wallafawa ranar:
Taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen Larabawa da musulmi na Duniya ya zo ne a wani lokaci da dakarun Isra'ila suka kashe mutane 11,000 galibi fararen hula da yawancinsu kananan yara, a cewar ma'aikatar lafiya ta Hamas.da dama a Gaza.
Shugabannin Gabas ta Tsakiya sun yi kira da a tsagaita wuta yayin da suke gargadin hadarin da ke tattare da rikici a wasu kasashe.
Hotunan da aka watsa a tashar Al-Ekhbariya sun nuna Shugaban Iran Raisi sanye da gyale na gargajiya na Falasdinu.
Saudiya mai rinjayen ‘yan Sunni da Iran mai rinjayen ‘yan Shi’a sun yanke alaka a shekarar 2016 bayan da aka kai wa ofisoshin jakadancin Saudiya hari a Iran a lokacin zanga-zangar nuna adawa da hukuncin kisa da Riyadh ta yi wa malamin Shi’a Nimr al-Nimr.
Sai dai a watan Maris din da ya gabata, wata yarjejeniya da kasar Sin ta kulla, ya sa abokan hamayyar da suka dade suna adawa da juna sun amince da maido da huldar diflomasiyya tare da sake bude ofisoshin jakadancinsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu