Isa ga babban shafi

Zelensky ya zargi Rasha da cusawa yaran Ukraine tsananin kiyayyar kasar

Shugaba Volodymyr Zelensky, ya zargi Rasha da cusawa kananan yaran Ukraine da ta sace tsananin kiyayya ga kasarsu, tare da kawo karshen duk wata alaka da ‘yan uwansu na jini.

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky.
Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky. AP - Seth Wenig
Talla

Zelensky ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78 da ke gudana a birnin New York.

00:54

Fassarar kalaman shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky

Shugaban na Ukraine dai ya dade yana caccakar Rasha akan kwashe dubban kananan yaran da take yi daga yankunan kasarsa da ta kwace, lamarin da ya sa kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC ta bayar da sammacin a kamo mata shugaban kasar Rasha Vladimir Putin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.