Isa ga babban shafi

Dumamar yanayi za ta fara lakume rayuka a duniya - IMF

Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF ya yi gargadin cewa matsalar dumamar yanayi na barazana ga matalautan kasashe, wanda idan har ba a dauki matakan gaggawa ba, za ta fara haifar da asarar rayuka nan da shekarar 2060. 

Yanayi gurbatacce
Yanayi gurbatacce AFP - TANG CHHIN SOTHY
Talla

IMF ya ce za a samu karuwar kaso 8.5 na adadin rayukan da za a yi asara, musamman a yankunan da ke fama da matsalar sauyin yanayi, kuma kaso 14 na wadannan kasashe za su fuskanci karuwar tsananin zafi. 

Daga cikin kasashe 39, wandanda ke dauke da kusan mutane biliyan guda na al’ummar duniya, rabi daga cikinsu da ke fama da wannan matsala sun fito ne daga nahiyar Afirka. 

Sama da mutum miliyan 50 ne a wadannan kasashe za su fuskanci tsananin yunwa a 2060, saboda kalubalen da ka iya dabaibaye hanyoyin samar da abinci da kuma hauhawar farashin kayayyaki. 

Hakan ta sanya IMF kira ga shugabannin kasashen duniya da za su gudanar da taro kan matsalar dumamar yanayin a kasar Kenya, domin samo mafita, musamman ga matalautan kasashe. 

IMF ya ce nan da shekarar 2040, wadannan kasashe za su iya fuskantar yanayin zafi sama da digiri 35 a ma'aunin celcius kwatankwacin na kwanaki 61 a shekara fiye da sauran kasashe. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.