Isa ga babban shafi

Bamu shirya shigar Ukraine cikin NATO a halin yanzu ba -Jen Stoltenberg

Duk da Bukatar da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ke da ita na Shiga kungiyar tsaro ta NATO, a karshe dai kungiyar ta ce har yanzu bata tsayar da tabbataccen lokacin da zata baiwa kasar damar shiga cikin ta ba.

Генеральный секретарь НАТО Йенс Столтенберг во время пресс-конференции в рамках саммита лидеров НАТО в Вильнюсе, Литва, 11 июля 2023 года.
Генеральный секретарь НАТО Йенс Столтенберг во время пресс-конференции в рамках саммита лидеров НАТО в Вильнюсе, Литва, 11 июля 2023 года. REUTERS - INTS KALNINS
Talla

Sai dai da ya ke jawabi ga manema labarai kan matsayar da aka cimma game da batun shigar Ukraine kungiyar ta NATO wanda shine ya mamaye taron, shugaban kungiyar Jen Stoltenberg ya ce babu tartibin lokacin da aka tsayar don baiwa Ukraine damar shiga NATO, amma dai da zarar ta kammala cika ka’idojin da ya kamata za’a sake duba yiwuwar hakan.

A cewar sa kasashe mambobin kungiyar zasu ci gaba da ganawa, a kuma fitar da dokoki da kuma Ka’idojin da ake bukatar Ukraine ta bi kafin sake duba yiwuwar chanchantarta wajen shiga kungiyar ko akasin hakan, sai dai har yanzu ba’a kai ga tsayar da lokacin da za’a fara fitar da ka’idojin ba.

Wannan matsaya dai ba ita ce shugaba Zelensky ya yi fatan a dauka ba, la’akari da yadda ya halarci taron na Lithuania da kwarin gwiwar cewa kungiyar ta NATO zata dauki mataki na karshe game da shigar kasar sa cikin ta, amma hakan bata samu ba.

Baki ya zo daya daga dukannin kasashe mambobin kungiyar, wadanda suka yi alkawarin baiwa Ukraine kariya daga mamayar Russia, ko da kuwa bai samu damar shiga NATO ba.

Dukannin alkawurran da kasashen suka dauka a yayin wannan taro, sun sha daukar makamancin su tun fara yakin sai dai da alama babu abinda ya sauya, duk da irin makaman da suke taimakawa Ukraine da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.