Isa ga babban shafi

Burundi ta bijire wa Majalisar Dinkin Duniya

Kungiyoyin fararen hula sun koka da matakin da gwamnatin Burundi ta dauka na ficewa daga zauren zaman nazartar kundinta na take hakkokin bil’adama  da Majalisar Dinkin Duniya ke jagoranta.

Shugaban Burundi, Évariste Ndayishimiye
Shugaban Burundi, Évariste Ndayishimiye AFP
Talla

Wannan dabi’ar da Burundi ta nuna ta jefa fargaba a zukatan kungiyoyin fararen hula da suka nuna damuwa kan yadda kasashen duniya ke bijire wa Majalisar Dinkin Duniya.

Lokaci zuwa lokaci, Majalisar Dinkin Duniya na gudanar da nazari kan yadda gwamnatocin kasashe ke mutunta dokokin kare hakkin bil’adama.

Sai dai a wani yanayi na ba-zata, tawagar wakilai 15 ta Burundi ta fice daga zaman da ta yi tare da Kwamitin Kare Hakkin Bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya a ranar Litinin da ta gabata a birnin Geneva saboda abin da ta kira “wasu miyagu da ke gabatar da kansu a matsayin mambobin kungiyoyin fareren hula.

Wannan dabi’ar da Burundi ta nuna, na zuwa ne bayan makamanciyarta da Nicaragua ta yi, wadda ta ki amincewa a yi zama da ita domin nazartar wata azabtarwa da ake zargin ta da aikatawa.

Kazalika ita ma kasar Rasha sau biyu tana kaurace wa irin wannan zama tare da Majalisar Dinkin Duniya a bara na nazartar wasu daga cikin ayyukanta da ake ganin laifi ne.

Majalisar Dinkin Duniyar ta nuna damuwa kan yadda kasashen duniya ke bijire mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.