Isa ga babban shafi

Taron Yanayi: Akwai bukatar sauyi a tsarin rance na duniya - Macron

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya bude taron tattauna hanyoyin da za a samar da kudaden yaki da sauyin yanayi a Alhamis din nan, inda ya ce akwai bukatar sauye sauye a tsarin bada rance na duniya domin tabbatar da cewa talauci bai kawo nakasu a yakin da kasashe marasa galihu ke yi da sauyin yanayi ba.

Shugaba  Emmanuel Macron,a yayin bude taron yanayi a Paris. 22 ga Yanayi`, 2023.
Shugaba Emmanuel Macron,a yayin bude taron yanayi a Paris. 22 ga Yanayi`, 2023. AP - Ludovic Marin
Talla

Ya ce tsarin bayar da rance na duniya da bankin duniya da asusun bada lamuni na duniya suka  samar da shi ya taimaka a shekarun baya, sai dai akwai alamun rashin dacewa da kalubalen zamanin yanzu.

Macron ya kara da cewa  zai yiwu a inganta tsarin ta inda zai tinkari tagwayen kalubale da suka addabi duniya, wato talauci da sauyin yanayi.

Ya ce akwai bukatar a samar da kudade tare da zuba jari a bangaren fasaha mara gurbata muhalli don taimaka wa duniya wajen sauyawa zuwa ayyukan tattalin arziki da ba sa lahani ga muhalli.

Macron yana karbar bakuncin wannan taro ne  tare da Fira ministan Barbados, Mia Mottley,  wanda ya kasance a kan gaba wajen da’awar neman bankin duniya da asusun bada lamuni na duniya su  sake fasalta alkiblarsu a wannan lokaci na sauyin yanayi.

Shugannin kasashen da ke halartar wannan taro sun hada da William Ruto na Kenya, shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz, Fira ministan China, Li Qiang da shugabar hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen.

Faransa tana karbar bakuncin wannan taro na kwanaki biyu ne a matsayin wata kafa ta tattauna wasu batutuwa gabanin taron tattalin arziki da na sauyin yanayi da ke tafe nan gaba a wannan shekarar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.