Isa ga babban shafi

Taron tallafa wa kananan kasashe ya gaza cimma abin da ake fata - MDD

Dalar Amurka biliyan 1.4 da aka tara a birnin Doha na kasar Qatar, a matsayin tallafi da kuma bashi da za a bawa matalautan kasashe, Majalisar Dinkin Duniya ta ce sun yi kadan ga matalautan kasashe.

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya kenan, Antonio Guterres.
Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya kenan, Antonio Guterres. REUTERS - AHMED SAAD
Talla

Babban Sakataren MDD, Antonio Guterres ya ce ana bukatar ninka adadin kudin da aka tara a wannan taro.

Wani babban wakilin Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin a karshen taron kwanaki biyar na kasashe mafi karancin ci gaba da aka yi cewa wadannan kasashe na samun koma-baya wajen cimma manufofin ci gaba.

Guterres ya bude taron ne da cewa kasashe 46 masu fama da talauci na bukatar dala biliyan 500 a duk shekara domin cimma muradun ci gaba mai dorewa na Majalisar Dinkin Duniya, wato tsarin da ya kasance na kawo karshen talauci da bunkasa kiwon lafiya da ilimi nan da shekarar 2030.

Daga cikin kasashen suka mika tallafi ko kuma basuka sun kunshi Saudiyya, Jamus, Kungiyar Tarayyar Turai, Qatar da kuma Canada.

Kasar Saudiyya dai ta yi alkawarin bayar da bashin Dala miliyan 800 ga matalautan kasashen.

Itama kasar Jamus ta ce za ta bayar da Dala miliyan 210, inda Kungiyar Tarayyar Turai ta yi alkawarin zuba jarin Dala miliyan 135 a wadannan kaashe.

Qatar mai masaukin baki, ta yi alkawin bayar da Dala miliyan 60, sai Canada dala miliyan 59, tare da bayar da tallafin magungunan da kuma bada gudun mow aga harkokin samar da ci gaba.

Mataimakiyar babban sakataren na MDD, Amina Muhammad, ta ce shirin na ci gaban muradun karni, ya shafi dukkanin kasashe kama daga matalauta zuwa masu karfin tattalin arziki, said ai ta ce matsawar manyan kasashe bas u agaza ba, to kuwa za a mayar da hannun agogo baya.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, babu wani shugaba daga manyan kasashen duniya da ya halarci wannan taro da aka shirya domin tallafawa matalautan kasashe.

Haka zalika, kasashe mambobin G20 basu bayyana yadda za su tallafawa kananan kasashen a babban taron na Majalisar Dinkin Duniya da ya gudana a Qatar din ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.