Isa ga babban shafi

Iran ta zartas da hukuncin kisa kan wasu mutane da aka samu da laifin yiwa Isra'ila aiki

Kasar Iran ta zartar da hukuncin kisa kan wasu mutane hudu tare da daure wasu mutane uku da ake zargi da yiwa kasar Isra'ila aikin leken asiri.

Shugaban Iran Ibrahim Ra'isi kenan lokacin da yake gabatar da jawabi yayin wani taro a Tehran ranar 4 ga watan Nuwamba.
Shugaban Iran Ibrahim Ra'isi kenan lokacin da yake gabatar da jawabi yayin wani taro a Tehran ranar 4 ga watan Nuwamba. AP - Vahid Salemi
Talla

Mutanen hudu da aka bayyana sunayensu da Hossein Ordoukhanzadeh, Shahin Imani Mahmoudabad, Milad Ashrafi Atbatan, da Manouchehr Shahbandi Bojandi, an rataye su ne da sanyin safiyar Lahadi.

Ma’aikatar shari’ar ta kira su da ’yan daba kuma ta ce jami’an leken asirin Isra’ila ne ke jagorantar su a lokacin da suke lalata dukiyoyin jama’a, sata, garkuwa da mutane da sauransu.

A cewar ma’aikatar shari’a, dukkan mutanen suna da tarihin aikata laifuka, masu alaka da Ordoukhanzadeh  wanda ake zargi da alaka da Mossad, mutumin da aka daure a kasar Girka tsakanin 2014 zuwa 2017 saboda yunkurin safarar mutane daga Turkiyya zuwa Girka.

An yi zargin cewa sun karbi kudade ne ta hanyar amfani da kudin dijital tare da sayen makamai da kayan aiki a lokacin da suke karbar horo kan yadda za su lalata na’urorin daukar bayanai, da musayar motoci, lamarin da ma'aikatar shari'ar Iran ta ce ya kara jaddada hakikanin yadda suke aiki karkashin ikon Mossad.

An mika tuhumar mutanen hudun ne ga kotun koli, wacce ta tabbatar da hukuncin da aka yanke a ranar Lahadi. A ranar Laraba ne dai hukumar shari'a ta sanar da yanke hukuncin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.