Isa ga babban shafi

Wasu nau'ikan dabbobi sun fara bacewa a duniya - WWF

Asusun kula da kuma kare lafiyar dabbobi na duniya, ya koka game da yadda adadin dabbobi ke ci gaba da raguwa, yayin da ake fargabar karewar wasu na’ukan dabbobi baki daya a duniya.

Goggon biri a wani gidan namun daji dake Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo
Goggon biri a wani gidan namun daji dake Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo © REUTERS - Reuters Staff
Talla

Asusun na WWF ya ce ayyukan dan adam, da kuma yadda yake ganganci wajen kula da yanayi da dazuka shine ummul,abaisin tilastawa dabbobin karewa saboda an  gurbata kyakyawan yanayin da zai basu damar gudanar da rayuwa mai inganci.

A cewar asusun wannan shine karo na farko da rahoton binciken sa ya nuna cewa an samu raguwar manyan dabbobi a duniya da kusan kaso 70 cikin 100, wanda kuma hakan abu ne mai tayar da hankali.

Ko da yake karatun baya, asusun na WWF a kididdigar nau’ukan dabbobi da yake da su guda dubu 32, yace a yanzu sama da dubu 5 sun kare a duniya wadanda suka hadar da dabbobi masu rarrafe, tsuntsaye da kuma kifaye.

Asusun ya kuma kara da cewa a yankuna irin su Latin Amurka da Karebiya lamarin ya fi muni, inda aka samu raguwar dabbobin da kaso 94 cikin dari.

Tun shekarar 1970 dai rahotanni suka bayyana cewa adadin dabbobin da ake da su a duniya ya ragu da kaso 69 cikin 100, amma a wannan karo an sami kari da kuma batun karewar su baki daya a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.