Isa ga babban shafi

Makabartar dabbobi zalla ta cika shekara 100 a Italiya

Yayin da ake ci gaba da bukukuwan cikar makabartar dabbobi irin ta ta farko a tarihi wacce ta ke a kasar Italiya shekaru 100 da kafuwar ta a bana, jama’ar kasar na ci gaba da tururuwa don kai ziyara ga dabbobin su da suka mutu daruruwan shekaru da suka gabata.

Makabartar dabbobi zalla kenan da ke kasar Italiya
Makabartar dabbobi zalla kenan da ke kasar Italiya © AFP
Talla

Wannan makabarta dai ta kasance wajen kwanciya na karshe ga dabbobin jama’ar Italiya, inda suke musu jana’iza da kuma binne su cikin kaburbura tare da sanya shaidar mutuwa da alamomi tamkar dai yadda ake yiwa kaburburan ‘yan adam.

Dabbobi irin su Maguna, Karnuka, Jakuna, Dawaki, Zomo da sauran dabbobin gida, na daga cikin wadanda ke samu wannan gata daga jama’ar Italiya ta hanyar yi musu jana’iza da kuma binne su cikin wannan makabarta, yayin da iyalai ke kai musu ziyara lokaci zuwa lokaci don nuna alhinin rashin su.

Guda daga cikin dabbobin shahararrun mutanen da aka binne a makabartar sun hadar da kazar tsohon shugaban kasar Benito Mussoloni, kuma cikin shekaru 100 da makabartar mai suna Casa Rosa ta kwashe an binne dabobbi sama da 1,000.

Bisa ala’adar al’ummar kasar dai akan yi wa dabbobin ado tare da binne su cikin kaburburan da suka sha ado da duwatsu na alfarma da furanni masu kamshi yayin da ake haka kaburburan kasarkashin bishiyar dabino don kare su daga shan zafin rana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.