Isa ga babban shafi

Jama'a sun fara gangami domin halartar jana'izar Sarauniyar Ingila

Shugaban Amurka Joe Biden zai yi gaisuwa ta karshe a birnin Landan ga Sarauniya Elizabeth ta biyu, yayin da aka gargadi mutanen da ke jira a layukan cewa lokaci ya kure don ganin akwatin gawarta.

Sarki Charles na uku kenan lokacin da yake nuna ban girma ga gawar mahaifiyarsa Sarauniya Elizabeth ta biyu
Sarki Charles na uku kenan lokacin da yake nuna ban girma ga gawar mahaifiyarsa Sarauniya Elizabeth ta biyu AFP - JANE BARLOW
Talla

Bayan da suka halarci taro a zauren majalisar dokokin Westminster, Biden, Sarkin Japan Naruhito da sauran shugabannin duniya sun halarci liyafa tare da Sarki Charles na III.

Biden, wanda ya tashi da yammacin ranar Asabar, ya ce mahaifiyar Charles "ta ajiye wani irin tarihi a zamani daban-daban" bayan da ta yi mulki na tsawon shekaru 70.

Firayim Ministan Australiya Anthony Albanese, wanda ya ziyarci inda akwatin gawar sarauniyar yake, ya bayyana ta a amtsayin mai tabbatar da gaskiya.

Hakanan sarkin ya gana da wasu bakin a Fadar Buckingham, ciki kuwa har da Firayim Minista Jacinda Ardern na New Zealand, wanda kamar Ostiraliya da sauran kasashen renon Ingila na Commonwealth 12 yanzu suna daukar Sarki Charles kamar yadda suka dauki Sarauniya Elizabeth ta biyu.

Tuni dai jama'a suka fara yin sansani domin kallon gagarumin bankwanan da za a yi a ranar Litinin a Westminster Abbey, wanda ake sa ran zai jawo hankali sosai a birnin Landan kuma biliyoyin mutane a duniya za su kalla ta kafar internet.

Jama'a kuma sun yi dafifi a kusa da fadar Windsor, da ke yammacin London, inda za a tuka akwatin gawar Sarauniyar, daga bisani kuma za a yi jana'izar ta inda aka yi na mijinta marigayi Yarima Philip, da iyayenta da kuma 'yar uwarta.

A yayin da masu ta’aziyya ke ci gaba da yin dafifi, Yarima William da kaninsa Yarima Harry sun jagoranci jikokin Sarauniyar guda takwas a cikin wani shirin girmamawa ga Sarauniyar inda suka kewaye akwatin gawar har tsawon dakika 12.

Harry wanda ya yi rangadi har sau biyu tare da Sojojin Burtaniya a Afganistan, ya sanya kakin soja tare da ‘dan ‘uwan nasa yarima mai jiran gado

Wannan shine karon farko da Yariman ya sanya kakin bayan barin masarautar shi da mai dakinsa Meghan tare da koma wa Arewacin Amurka, sakamakon zargin masarautar da nuna wariyar launin fata.

Za a yi bikin jana'izar Sarauniya Elizabeth, wanda shi ne na farko a Biritaniya tun bayan mutuwar firaministanta na farko Winston Churchill a shekarar 1965, a ranar Litinin a Westminster Abbey da karfe 11:00 na safe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.