Isa ga babban shafi

Duniya na alhinin tunawa da gimbiya Diana bayan shekaru 25 da mutuwarta

An haifi Gimbiya Diana Frances Spencer a ranar 1 ga watan Yulin 1961 a park house kusa da Sandringham, Norfolk na kasar Ingila, kuma itace auta cikin jerin ‘ya’yan Viscount da Viscountess Althorp.

Wani wuri da mutane ke taruwa don tunawa da cika shekaru 25 da rasuwar gimbiya Diana Spencer a ranar 31 ga Agusta, 2022 a Faransa.
Wani wuri da mutane ke taruwa don tunawa da cika shekaru 25 da rasuwar gimbiya Diana Spencer a ranar 31 ga Agusta, 2022 a Faransa. AFP - EMMANUEL DUNAND
Talla

Gimbiya Diana dai ta yi karatun firamaren ta a Riddlesworth Hall a Diss dake Norfolk, daga bisani kuma ta wuce makarantar kwana ta West Health a shekarar 1974.

Bayan kamala karatuttukan ta, Gimbiya Diana ta kuma fara aiki a Birnin London a matsayin mai renon yara, da kuma aikin girki, kafin daga bisani kuma ta koma aiki a wata makarantar yara ta Young England Kindergaten duk dai a birnin na Landan.

A wannan tsukun ne kuma aka fara yada jita-jitar bullar alakar soyayya tsakanin ta da Yarima Charles, inda kuma idanun duniya suka koma kanta.

A ranar 24 ga watan Fabrairun 1981 ne aka sanar da baikon Yarima Charles da Lady Diana Spencer a fadar Buckhingham, inda kuma liyafar ta lakume yawan kudade har Fam dubu 30, a wancan lokacin, dai-dai da Fam dubu 36 na yanzu.

Zoben da yarima Chales ya bata a wancan lokaci ya zama abin magana a tsakanin jama’a saboda tsadar sa, yayin da yake dauke da lu’ulu’u har goma sha hudu a jikin sa.

Bayan watanni biyar da baikon ne kuma aka daurawa masoyan biyu aure a ranar 29 ga watan Yulin 1981 a majami’ar St Paul Cathedral, yayin da ake ganin bikin nasu yafi kowanne kayatarwa a wancan karnin.

Bayan shekara guda da auren ta ne kuma ta haifi dan ta na farko a ranar 21 ga watan Yulin 1982 wato Prince William, wanda shine na biyu cikin jerin wadanda zasu gaji sarautar ingila.

Gimbiya Diana ta sake haihuwar da Namiji a ranar 15 ga watan Satumbar 1984, yayin da aka sa masa suna Henry, amma an fi saninsa da Yarima Harry.

A wata ziyara da Gimbiyar ta kai Amurka ta yi rawa da wani jarumin Film John Travolta a fadar White House, abinda ake alakantawa da irin sunan da ta yi da kuma yadda ta ke jan hankalin jama’a da yanayin suturun kawa da alfarma da take sawa, kuma ana zargin wannan shine mafarin rashin jituwa tsakanin ta da mai gidan ta.

Ayyukan jin kan da ta ke yi ya kara janyo mata soyayya a zukatan jama’a, yayin da ta taka rawa sossai a rayuwar mutanen da ke fama da cuta mai karya garkuwar jiki a wancan lokaci.

A shekarar 1992 ne aka fara fuskantar zaman doya da manjar da masoyan biyu ke yi, bayan wata tafiya da gimbiyar ta yi zuwa India ita kadai, abinda ba’a saba gani ba.

Bayan kuma shafe tsahon shekaru ana zaman rashin jituwa a tsakanin ma’auratan ne kuma a karshe Yarima Charles ya saki gimbiya Diana a ranar 28 ga watan Agustan 1996.

An fara zargin soyayya ta shiga tsakanin ta da Dodi Al Fayed dan hamshakin attajirin nan Mohammed Al-Fayed, bayan hango su da aka yi sun shiga mota tare da barin wajen taron liyafar cin abincin dare da aka shirya a birnin Paris.

Fitar su ke da wuya ne kuma masu daukar hotuna suka rika binsu akan babura abinda ya sanya suka tafka mummunan hadari a wani titi da ke karkashin gada, lamarin da ya yi sanadin mutuwar ta, tana da shekaru 36.

Mutane sama da miliyan biyar ne dai suka yi jerin gwano a wajen jana’izar ta, kuma har yanzu ana tunata cikin shauki da bege duk da ta shafe shekaru 25 da rasuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.