Isa ga babban shafi

Fafaroma ya nemi afuwa kan ci zarafin da aka yi wa yara

Fafaroma Francis ya nemi afuwa mai cike da tarihi gurin iyalai da daliban da suka ci karo da cin zarafi a kwalejojin ‘yan darikar Katolika da ke Canada, a wani al’amari na farko da ya gudanar a ziyarar mako guda da yake yi a Canada.

Fafaroma Francis da ke ziyara a Canada
Fafaroma Francis da ke ziyara a Canada REUTERS - GUGLIELMO MANGIAPANE
Talla

Neman afuwar ya zama irinsa na farko a tarihi da Fafaroma Francis ya yi ga wadanda suka ci karo da cin zarafi a kwalejojin daga malamansu sama da shekaru 30 da suka gabata.

Tuni dai jagoran mabiya darikar Katolikan sama da biliyan 1 da miliyan 300 a duniya ya isa yankin Edmonton da ke gundumar Alberta na Canada, don ziyarar kwaleji ta farko da aka fara samun rahoton cin zarafin ta hanyar fyade.

An dai shirya ziyarar shugaban ‘yan Katolikan mai shekaru 85 kawai don neman afuwar a laifin aikata cin zarafin ta hanyar fyaden da aka kwatanta da Kisan mummuke.

Bayanan da gwamnatin Canada ta tattara na nuna cewa, daga tsakanin shekarun 1980 zuwa 1990, an samu rahoton cin zarafin yara ta hanyar fyade guda dubu 150 a makarantun katolika 139, tare da kaste duk wata alaka tsakaninsu da iyayensu da kuma hana su gudanar da al’adu da kuma amfani da yarensu.

Al’amarin bai tsaya iya kan dalibai ba, har ma da malamai, yayin da wasu suka rasa rayukansu a dalilin cututtuka rashin kulawa da kuma yunwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.