Isa ga babban shafi
Rasha-Ukraine

Duniya na cikin hadarin fuskantar karancin abinci saboda yakin Ukraine- MDD

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi gargadi kan yadda yakin yakin Rasha a Ukraine ke kokarin jefa duniya a matsalar kamfar abinci saboda yadda rikicin zai hana noma a sassan duniya.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres yayin jawabi gaban manema labarai a birnin New York bayan kammala zaman kwamitin tsaro kan rikicin Rasha da Ukraine.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres yayin jawabi gaban manema labarai a birnin New York bayan kammala zaman kwamitin tsaro kan rikicin Rasha da Ukraine. REUTERS - CARLO ALLEGRI
Talla

A jawabinsa gaban manema labarai a birnin New York, Guterres ya ce duniya za ta fada halin tsaka mai wuya sanadiyyar guguwar yunwa da tsadar kayakin abinci sakamakon rikicin na gabashin Turai.

Guterres ya ce farashin kayakin abinci zai yi tashin da duniya bata taba gani ba matukar ba a dauki matakan da suka kamata ba inda a yanzu haka kasashe da dama ciki har da na Afrika suka fara dandana kudarsu.

Akalla kasashe 45 da suka kunshi wasu a nahiyar Afrika da kuma wasu masu tasowa ne suka dogara da Rasha da Ukraine wajen shigo da tan tan na alkama kuma 18 daga cikin sun dogara ne kacokan wajen samun kashi 50 na abincinsu daga kasashen biyu.

Kasashen da suka kunshi Yemen da Lebanon da Libya da Sudan da kuma Somalia baya ga Burkina Faso da Masar da kuma Jamhuriyar Demokuradiyar Congo su ne 'yan gaba gaba da suka dogara da Ukraine da Rasha wajen samun alkama.

Magatakardar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce dole ne mahukunta su mike tsaye don lalubo hanyoyin warware rikicin na Rasha da Ukraine da nufin ceto duniya daga bala'in guguwar yunwa.

Kwanaki 20 kenan cif da Rasha ta fara mamaya a Ukraine wanda ya kai ga rasa rayukan dimbin fararen hula baya ga dubunnan dakaru daga kowannen bangare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.