Isa ga babban shafi
Faransa

Shugabannin duniya na taron zaman lafiya a Paris

An bude taron samar da zaman lafiya da ke hada shugabanin kasashen duniya a birnin Paris na Faransa, taron da ake kyautata zaton zai taimaka wajen samar da hanyoyin warware wasu daga cikin tarin matsallolin da suka addabi duniya.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, Mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a taron na zaman lafiya a birnin Paris.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron, Mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a taron na zaman lafiya a birnin Paris. © Nigeria presidency
Talla

Shugabannin za su shafe tsawon kwanaki uku suna tattaunawa dangane da batutuwa da dama da suka hada da muhalli da lafiya da na'urar zamani.

Daya daga cikin batutuwan da zai fi daukar hankulan shugabanin shi ne na tantance hanyoyin kawo karshen annobar cutar Covid19.

Daga cikin shugabanin kasashen da ake sa ran za su bada gagarumar gudunmawar magance matsalolin har da shugaban Senegal Macky Sall da shugaba Mohammadu Buhari na Najeriya da mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Haris. Sai mai masaukin baki Emmanuel Macron.

Ana kyautata zaton mutane  dubu 15 za su kasance kai tsaye ta intanet domin kallon irin wainar da za a tuya a taron, yayin da mutane 350 za su kasasne a zauren taron kuma daga cikinsu har da shugabanin kasashen Ddniya 30, 12 daga Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.