Isa ga babban shafi
Nobel

'Yan jarida sun lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel

Fitacciyar ‘yar jaridar Philippines Maria Ressa da takwaranta na Rasha Dmitry Muratov sun lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel saboda gwagwarmayarsu ta tabbatar da ‘yancin fadin albarkacin baki a daidai lokacin da demokuradiya ke fuskantar barazana.

Dmitry Muratov da Maria Ressa da suka lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel
Dmitry Muratov da Maria Ressa da suka lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel AP - Mikhail Metzel/Aaron Favila
Talla

Ressa na cikin wadanda suka yi hadin guiwa wajen kafa dandalin aikin jarida na yanar gizo mai suna Rappler a Philippines, inda suke mayar da hankali kan bincike-bincike , yayin da Muratov na Rasha, shi ma suka yi hadin guiwa wajen kafa jaridar Novoya Gazeta mai zaman kanta.

An dai karrama gwarazan biyu ne saboda jajircewarsu wajen kare ‘yancin fadin albarkacin baki, wanda ke matsayin tubalin farko na gina demokuradiya da kuma samun zaman lafiya mai dorewa kamar yadda shugabar kwamtimin Nobel, Berit Reiss-Andersen ta bayyana.

Reiss-Anderson ta kara da cewa, wadannan mutane biyu, sun wakilci daukacin ‘yan jaridar da suka yi tsayin daka wajen tabbatar da ‘yancin fadin albarkacin baki a wannan duniyar.

Ressa mai shekaru 58 ta ce, kyautar ta Nobel da aka mika mata, ta nuna cewa, babu wani abu da zai tabbata ba tare da hujjoji ba, tana mai alakanta demokuradiya da ‘yancin fadin albarkacin baki.

‘Yar jaridar ta yi fice wajen sukar lamirin shugaban Philippines Rodrigo Duterte.

Shi kuwa Murartov na Rasha ya sadaukar da rabin kyautar ta Nobel ga abokan aikinsa da suka rasa rayukansu tun daga shekara ta 2000, cikinsu kuwa har da fitacciyar ‘yar jaridar nan mai binciken kwa-kwafa Anna Politkovskaya.

Tuni fadar gwamnatin Rasha ta Kremlin ta taya shi murnar samun wannan kyauta, tana mai cewa, dan jarida ne mai hazaka da jajircewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.