Isa ga babban shafi
Pandora Papers

Shugabannin duniya sun mayar da martani kan 'Pandora Papers'

Sakamakon fitar da wasu mahimman takardu da ke bayyana yadda dimbim fitattun mutane a duniya suka boye tarin dukiyoyi da suka kai miliyoyin Dala a asusun ajiyar kasashen ketare da babu haraji, gwamnatoci sun yunkuro don rage tasirin wannan tonon sililin na binciken da aka yi wa lakabi da ‘Pandora Papers’.

Sama da 'yan jarida 600 ne suka tattara bayanai kan tonon sililin bayan gudanar da bincike a kasashen duniya 117
Sama da 'yan jarida 600 ne suka tattara bayanai kan tonon sililin bayan gudanar da bincike a kasashen duniya 117 LOIC VENANCE AFP
Talla

Sunayen wasu shugabannin 35, tsaffi da masu ci ne suka bayyana a  wasu kundaye da suka kai akalla miliyan 11 da dubu 900 da aka bankado daga cibiyoyin kudi a  fadin duniya wanda aka  yi wa lakabi da ‘Pandora Papers’.

Cikin wadanda sunayensu suka bayyana a wandannan kundaye ,akwai tsohon Fiiraministan Birtaniya, wanda aka nuna ya kauce wa biyan harajin kan wani gidansa na birnin Landan.

Babu sunan shugaban Rasha Vladimir Putin, amma kuma an danganta shi da wasu kadarori na makusantansa  a birnin Monaco na Faransa, musamman wani gida na kusa da teku, mallakin wata mata da suka haihu da ita.

 Sai dai kakakin fadar Kremlin ta Rasha, Dmitry Peskov ya ce, zargi ne mara tushi.

Ita ma Jordan ba ta yi kasa  a gwiwa ba wajen yin watsi da rahoton cewa ,an bankado tarin kadarori da suka kai miliyan 100 na Dala da Sarki Abdallah na biyu ya tara a California da Landan.

Cibiyar ‘yan jarida ta kasa da kasa ta gudanar da wannan bincike, wanda kafofin yada labarai da suka hada da Washington Post, BBC da Guardian suka watsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.