Isa ga babban shafi

Yan Sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a Bangkok

Yan Sandan Thailand a jiya asabar sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye tareda harba albarusai na roba wajen tarwatsa dubban masu zanga-zanga da kuma adawa da manufofin gwamnatin dake rike da mulki a kasar.

Masu zanga-zanga  a Thailand
Masu zanga-zanga a Thailand AP - Sakchai Lalit
Talla

Masu boren na bayyana cewa babu abinda hukumomin suka yi yanzu haka a mataki na dakile yaduwar cutar covid 19 inda alkaluma ke dada nuni cewa kusan mutane 22.000 ne suka kamu da ita a Thailand, 212 sun bakuci lahira.

Yan Sanda na tarwatsa masu zanga-zanga a Bangkok
Yan Sanda na tarwatsa masu zanga-zanga a Bangkok © Anuthep Cheysakron/AP

A daya geffen masu bore na kokawa dangane da tafiyar hawainiya da  ake fuskanta wajen yiwa mutane allurar rigakafin kamuwa da wannan cuta,a karshe sun kuma bukaci Firaministan kasar da yayi murabis.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.