Isa ga babban shafi
Duniya - Coronavirus

Adadin mutanen da suka kamu da Korona ya haura miliyan 200

Adadin mutanen da suka kamu da cutar Korona a duniya ya haura miliyan 200, kamar yadda alkaluman da kamfanin dillancin labarai na AFP ya tattara suka nuna a ranar Alhamis.

Tsiwairar duniya da na'urar Komfuta ta fitar da ke nuna misalin yadda annobar Korona ke kara mamaye sassan duniyar.
Tsiwairar duniya da na'urar Komfuta ta fitar da ke nuna misalin yadda annobar Korona ke kara mamaye sassan duniyar. © 网络照片 Getty Images/iStockphoto - ismagilov
Talla

Rahoton na zuwa ne a daidai lokacin da China ta yi alkawarin bayar da tallafin alluran rigakafin cutar Kornar biliyan biyu a wannan shekara, domin dakile sake yaduwar da annobar ke yi cikin sauri, sakamakon bullar sabon nau’inta mafi hatsari na Delta.

Nahiyar Asiya da Pacific ke kan gaba wajen fuskantar barazanar sabon nau’in Koronar na Delta, inda a Thailand, Indonesia da Japan adadin masu kamuwa da cutar ke karuwa a kullum, yayin da kuma a Australia tuni al’ummar birnin Melbourne suka sake shiga kullen takaita zirga-zirga.

Masu wucewa sanye da kyallen rufe fuska yayin tsallaka yankin Shibuya  da ke birnin Tokyo a kasar Japan. 23/4/2021.
Masu wucewa sanye da kyallen rufe fuska yayin tsallaka yankin Shibuya da ke birnin Tokyo a kasar Japan. 23/4/2021. REUTERS - KYODO

Sabbin alkaluman hukumomin lafiya sun nuna cewa adadin masu kamuwa da cutar Korona kowace rana a fadin duniya ya haura kashi 68 cikin 100 tun daga tsakiyar watan Yuni kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.

A Thailand, a karon farko yawan karin mutanen da suka harbu da Korona ya kai dubu 20 cikin sa’o’i 24 a ranar Laraba, adadin da ya sake maimaituwa a ranar Alhamis.

A Indonesia kuwa, adadin wadanda cutar Korona ta kashe ya haura dubu 100 jumilla a ranar Laraba, bayan samun karin mutane dubu 1 da 739 da annobar ta lakume daga cikin asarar rayuka dubu 10 da 245 da aka yi a fadin duniya cikin sa’o’i 24.

Kawo yanzu mutane miliyan 4 da dubu 250 suka rasa rayukansu a fadin duniya dalilin Korona, tun bayan barkewarta daga China a watan Disambar shekarar 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.