Isa ga babban shafi
Bosnia-ICC

Kasashen duniya sun ji dadin hukuncin ICC kan Mladic

Majalisar Dinkin Duniya da wasu gwamnatocin kasashe, sun yaba da hukuncin kotun ICC na goyon bayan daurin rai-da-rai da aka yi wa tsohon kwamandan ‘yan tawayen Bosnia Ratko Mladic wanda ya yi wa Musulmi dubu 8 kisan kare-dangi.

Ratko Mladic
Ratko Mladic UN-IRMCT/AFP
Talla

Shugabar Hukumar Kare Hakkin Bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya Michelle Bachelet ta yi lale marhabin da matakin kotun ICC na yin watsi da karar da Mladic ya daukaka domin kalubalantar hukuncin daurin rai-da-rai da aka yi masa saboda aikata laifukan yaki a shekarar 1992-1995 a Bosnia.

Bachelet ta ce, hukuncin ICC na nuni da kudirin kotun na tabbatar da adalci komin dadewar laifin da aka aikata, kamar Mladic wanda ya aikata laifin kusan shekaru 30 da suka gabata.

Shugaban Amurka Joe Biden a nasa bangaren ya ce, shari’ar da kotun ta yi, manuniya cewa, za a rika gurfanar da mutanen da ke aikata miyagun laifuka, kuma hakan ya karfafa manufar da ake da ita ta hana aukuwar irin laifin nan gaba a ko’ina a fadin duniya.

Ita ma Jamus ta yi jinjina ga alkalan kotun, inda Ministan Harkokin Wajenta, Heiko Maas ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa, ya samu nutsuwa da hukuncin na kotun Hague.

Kazalika Ministan ya yi fatan cewa, matakin na kotun zai kwantar da hankulan iyalan mutanen da lamarin ya rutsa da su.

Kisan kare dangin da aka yi wa mutane dubu 8 akasarinsu maza musulmai da kuma yara, shi ne mafi muni da aka gani a nahiyar Turai tun bayan yakin duniya na  biyu.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.