Isa ga babban shafi
ICC-Bosnia

ICC ta ki amincewa da bukatar makashin Bosniyawa

Kotun Hukunta Manyan Laifuffuka ta ICC ta yi watsi da bukatar tsohon kwamandan 'yan tawayen Bosnia Ratko Mladic na neman sauya hukuncin da aka masa na daurin rai da rai sakamakon samun sa da laifuffukan yaki dangane da rawar da ya taka wajen kashe Bosniyawa Musulmi maza 8,000 a Srebrenica a shekarar 1995.

Bosnie Ratko Mladic
Bosnie Ratko Mladic AP - Jerry Lampen
Talla

Wannan hukunci na yau ya nuna cewar Mladic zai ci gaba da zama a gidan yari har iya ransa kamar yadda hukuncin kotun na shekarar 2017 ya bayyana.

Kisan mutanen da ya faru a yankin da ke karkashin kulawar Majalisar Dinkin Duniya shi ne mafi muni a nahiyar Turai bayan yakin duniya na biyu.

Mladic ya ki amincewa da hukuncin kotun na shekarar 2017, abin da ya sa shi daukaka kara domin ganin alkalan kotun sun sauya hukuncin.

Tsohon kwamandan da ake yi wa lakabi da ‘Mahauchin Bosnia‘ na daga cikin wadanda ake zargi na karshe da suka gurfana a gaban kotun duniya domin amsa tambayoyi dangane da kisan kare dangin da aka yi a Bosnia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.