Isa ga babban shafi
Coronavirus

Karnuka kan iya gano sama da kashi 90 na masu dauke da cutar korona - Bincike

Wani bincike da aka gudanar  ya gano cewa za’a'iya horar da karnuka don gano sama da kasha 90 cikin 100 na masu dauke da cutar korona ko da kuwa marasa lafiyan basu nuna alamun cutar ba, matakin da masu binciken ke fatan zai iya taimakawa maye gurbin bukatar killace jama’a bayan sun isa wata kasa.

Kare da aka horor don gano masu dauke da cutar coronavirus, 21 ga watan Mayu 2021.
Kare da aka horor don gano masu dauke da cutar coronavirus, 21 ga watan Mayu 2021. REUTERS - JORGE SILVA
Talla

Allah yayiwa karnuna wata baiwa na sinsina abu, kuma su gano daga kamshi ko warinsa, wanda masana suka kwanta da rabin ƙaramin cokali na sukari a cikin ruwan dake da girman karamin tafkin ninkaya na wasannin Olympics – Inda karnuka sukan gano cututtuka irin su kansar, zazzabin cizon sauro da kuma farfadiya.

Yayin da wasu bincike da suka gabata suka nuna hujja-ra'ayi cewa karnuka na iya gano SARS-CoV-2.

Yadda masana suka gwada karnuka

Masu bincike daga Makarantar harhada magunguna na London Tropical Medicine sun tattaro samfurar kayayyakin dubban mutanen da aka tabbatar suna dauke da cutar korona, kamar su safa da Kellen rufe hanci da baki, inda kuma karnukan suka iya gano kashi tsanakin 94 zuwa 82 cikin 100 da ke da cutar, har da mutanen da ba su nuna alamomin kamuwa da cutar ba. 

Masanan sunyi ittafakin yadda wannan zai ba da damar yin amfani da karnukan a wurare kamar filayen jiragen sama don tantance matafiya na iya gano kashi 91 cikin 100 na masu dauke da cutar, wanda hakan ke haifar da raguwar saurin yaduwa fiye da gwajin PCR kadai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.