Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya dakushe kimar Amurka a duniya-Obama

Tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya caccaki Donald Trump saboda abin da ya kira gazawarsa wajen jagorancin kasar da kuma kasa daukar aikinsa da muhimmaci kamar yadda dimokiradiya ta dora masa.

Shugaba Donald Trump na Amurka tare da Barack Obama
Shugaba Donald Trump na Amurka tare da Barack Obama AFP
Talla

Obama ya ce Trump ya dakushe kimar Amurka a duniya wajen neman biyan bukatar kansa da abokansa.

"Na zauna a ofishin shugaban kasa da mutane biyu da ke neman shugabanci kasa. Ban taba tunanin wanda ya gaje ni ba zai rungumi manufofi na ba, ko kuma ci gaba da aiwatar da aikin da muke yi." inji Obama.

Tsohon shugaban ya kara da cewa, ya yi fatar Donald Trump na iya nuna wata sha’awa ta daukar aikinsa da muhimmanci, amma ya gaza sauke nauyin da tsarin dimokuradiya ya dora masa.

Obama ya ce, kusan shekaru 4  kenan da Trump ya nuna rashin kula wajen gudanar da aikinsa, inda ya yi watsi da hanyoyin kawo ci gaba a Amurka.

"Ba ya sha’awar kawo ci gaba a ofishinsa na shugaban kasa, sai dai wasan kwaikwayon da yake yi domin dauke hankalin jama’a." inji Obama.

Wannan na zuwa ne a yayin da ake shirin gudanar da zaben shugaban kasa a cikin watan Nuwamba mai zuwa, inda Joe Biden na jam'iyyar Democrat zai fafata da Donald Trump na Republican.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.