Isa ga babban shafi
Duniya

Attajirai 26 kadai sun mallaki dukiyar da za ta ishi rabin al'ummar duniya - Guterres

Sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres, yace annobar COVID-19 ta bayyanar da matsalar rashin daidaiton dake tsakanin nahiyoyi, kasashe, da kuma yankunan duniya, yanayin da babban magatakardan yayi gargadin cewar, ka iya jefa mutane miliyan 100 cikin kangin talauci.

Antonio Guterres, Sakataren Majalisar Dinkin Duniya.
Antonio Guterres, Sakataren Majalisar Dinkin Duniya. REUTERS/Lisi Niesner
Talla

Guterres ya yi wannan gargadi ne, yayin jawabi wurin taron tunawa da cikar marigayi Nelson Mandela, tsohon shugaban Afrika ta Kudu cika shekaru 102 da haihuwa.

Sakataren majalisar dinkin duniyar yace hamshakan attajirai 26 kadai sun mallaki dukiyar da za ta ishi rabin yawan al’ummar duniya, abinda yace na daya daga cikin dalilan da suka haifar da rashin daidaito tsakanin al’umma.

Guterres ya kuma bayyana wariyar launi da kuma tsarin rashin adalci a tsakanin gwamnatoci, a matsayin wasu manyan illolin dake barazanar jefa karin miliyoyin mutane cikin talauci a sassan duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.