Isa ga babban shafi
Isra'ila-Falasdinu

Kasashen Faransa Jamus Jordan da Masar sun gargadi Isra'ila kan Falasdinu

Kasashen Faransa Jamus Jordan da Masar sun gargadi gwamnatin Isra’ila game da sabon shirinta na ci gaba da mamayar yammacin gabar tekun Jordan, kan cewa matakin mamayar matsugunan Falasdinawan ka iya shafar huldar diflomasiyyar da ke tsakaninsu.

Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu
Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu Gali Tibbon/Pool via REUTERS
Talla

Sanarwar da ministocin wajen kasashen 4 na Masar Jordan Jamus da Faransa suka fitar a yau Talata, ta ce matukar Isra’ilan ta ci gaba da mamayar Matsugunan na Falasdinawa wanda ya sabawa dokokin kasa da kasa don tabbatar da zaman lafiyar yankin da aka gindaya a shekarar 1967 ko shakka babu za su dauki tsattsauran matakin da bazai yiwa kasar dadi ba.

A cewar sanarwar duk wani yunkurin mamayar yankin na yammacin gabar kogin Jordan kai tsaye ya sabawa kokarin duniya ta samar da zaman lafiyar gabas ta tsakiya.

Gwamnatin Isra’ila dai karkashin Firaminista Benjamin Netanyahu ta sanar da shirin ci gaba da mamayar yankin da zai fara daga ranar 1 ga watan Yuli ko da dai shirin bai fara ba, haka zalika fadar gwamnatin ba ta fitar da sanarwa kan batun ba, wanda ya samu goyon baya daga shirin zaman lafiyar gabas ta tsakiya da Donald Trump ya gabatar farkon shekarar nan da ya fuskanci kakkausar suka daga shugabannin duniya.

Sanarwar hadakar kasashen wadda ta fita ta ma’aikatar wajen Jamus, ta ce ko kadan baza su aminta da samar da sauyi cikin yarjejeniyar 1967 da ta kayyade iyakar yankunan biyu na Isra’ila da Falasdinu ba, kuma yunkurin kalubalantar hakan zai tilasta mayar da martani.

Ko a makon jiya kungiyar Tarayyar Turai ta caccaki matakin Isra’ilan tare da yi mata barazana matukar ta aikata shirye-shiryen da ke kunshe cikin shirin zaman lafiyar Donald Trump da kungiyar ta bayyana a matsayin babbar barazanar tsaro da zaman lafiyar gabas ta tsakiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.